Wani rahoto da muka samu ya tabbatar da cewa hukumar EFCC sun kama Akanta Janar na tarayyar Najeriya, Ahmed Idris.

An kama akanta janar ɗin kan zargin almundahanar kuɗi da karkatar da kuɗin gwamnati.

Waɗanda suke da masaniya kan lamarin sun ce jami’an EFCC na Kano ne suka kama Ahmed Idris a yammacin ranar Litinin kuma za a tafi da shi Abuja domin amsa tambayoyi.

Majiyoyi sun ce EFCC ta daɗe tana bincike a kan zargin karkatar da Naira biliyan 80 na kuɗin gwamnati ta hanyar wasu kwangiloli na bogi.

Masu binciken sun ce an gano cewar kamfanonin da aka yi amfani da su wurin karkatar da kuɗin suna da alaƙa da ƴan uwan Akant Janar ɗin da abokansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: