Ana zargin wasu ƴan acaɓa da cinnawa wani matashi wuta a jihar Legas.

Matashin mutumin mai suna David, an yi masa dukan tsiya sannan aka cinna masa wuta wacce tayi sanadiyyar ajalin sa.

Ana zargin cewa David ya samu saɓani ne da wani ɗan acaɓa kan canjin naira 100, wanda hakan ya sanya faɗa barkewa tsakanin David da ɗan acaɓan.

Sauran abokan aikin ɗan acaɓan sun shiga cikin rigimar inda su ka yiwa David dukan tsiya har sai da ya sume.

David, yana kan hanyar sa ta komawa gida daga wajen shaƙatawa lokacin da lamarin ya auku a yankin Lekki Phase 1, jihar Lagos.

Wasu shaidun gani da ido sun ɗauki faifan bidiyo na abin da ƴan acaban suka yi a wurin.

Sanya faifan bidiyon da akayi a shafin Twitter ya nuna David a kwance a ƙasa da tayar mota na ci a jikin sa, lamarin daya ja
Mutane su ka fusata suka buƙaci a ɗauki mataki akan wanɗanda su ka aika hakan.

Bidiyo ya nuna yadda mutanen su ka sanya wa wutar man fetur, wanda hakan ya sanya wutar ta ƙaru.

David dai ya sha kashi ne tare da wasu abokan sa a hannun mutanen da har yanzu ba’a san ko su waye ba.

Abokan David, ma su suna Frank da Philip ana duba lafiyar su a wani asibiti da ba’a bayyana sunan sa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: