Mai magana da yawun shgaban kasa Muhammad Buhari kan kafafan yada Labarai Femi Adesina,ya bayyana cewa daga shekarar 2023 lokacin da wa’adin mulkin su ya kare zai koma ya ci gaba da gudanar da ayyukan gona da kuma harkokin kafafan yada labarai.

Adesina ya sanar da hakan ne a yau Alhamis a shafin sa na Facebook.

Femi ya yi furucin ne a lokacin da wata kungiyar Manoman Najeriya AFAN reshen Jiihar Edo ta kai masa ziyara.

Adesina ya ce a lokacin da kungiyar manoman ta kai masa ziyara sun nadashi a matsayin shugaban kungiyar.

Yakara da cewa bayan aikin noma zai cigaba da gudanar da ayyukan sa na kafafen yada labarai.

A yayin ziyarar ta kungiyar manoma Adesina ya nuna farin cikin sa a lokacin ziyarar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: