Al’ummar ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa a jihar Kaduna sun bayyana cewar da yawa daga cikin garuruwan da ke ƙananan hukumomin na ƙarkashin ikon ƴan bindiga.

Wani shugaba a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ya bayyana cewar ƴan ƙungiyar Ansaru sun mamaye wasu da yawa daga cikin garuruwa ƙanana hukumomin biyu na jihar.

Zubairu Abdulrauf ya shaida cewar ƴan bindigan da ake zargi mayaka ne daga ƙungiyar da ke iƙirarin jihadi ta Ansaru na gudanar da sintiri a wasu garuruwan cikin kayan jai’an tsaro.

Zubair Abdulra’uf ya ce daga cikin garuruwan da ƴan ƙungiyar Ansaru su ka mamaye akwai Kidandan, Kadage, Galadimawa, Yakawada.

Ya ce ƴan ƙungiyar Ansaru na kulawa da yakunan domin kare su daga hare-haren masu garkuwa da mutane.

Ya ƙara da cewa a halin da ake ciki mutanen yankunan na cikin kwanciyar hankali tun bayan da ƴan ƙungiyar Ansaru su ka fara ba su tsaro don kare rayuwa da lafiya da dukiyoyinsu.

Gwamnatin jihar ta bayyana a baya cewar, ƴan ƙungiyar Ansaru ne su ka kai hari kan jirgin ƙasa a Kaduna wanda har yazu akwai wasu mutane da ke hannunsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: