Masu hayar babur a jihar Legas sun roƙi gwamnatin jihar ta sasdauta musu dokar hana hayar babura a ƙanann hukumomi shida da wasu titunan jihar.

Shugaba ƙungiyar Musa Haruna Gazama ya bayyana cewar bayan hana hayar baburan da gwamnatin ta yi da yawa daga cikin masu tuƙa baburan sun bar jihar wasu kuma sun koma wasu ƙanann hukumomin da ba a haramta ba.

An haramta tuƙa babura a wasu yankunan jihar Legas bayan zargin hallaka mutum a kan naira 100.

Wasu labarai da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna cewar wasu daga cikin masu Achaɓa a jihar na shitin gudanar da zanga-zanga ranar 1 ga watan Yuni.

Sai dai rundunar ƴan sandan jihar ta haramta duk wata zanga-zanga da ake shirin yi.

Kwamishinan ƴan sandan jihar ya tabbatar da cewar ba za su saurarawa duk wamda su ka samu da karya doka ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: