Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta tabbatar da ɓullar cutar ƙyandar biri a Najeriya.

Hukumar tace an gano masu ɗake da cutar tun daga ranar 1 ga watan Janairun sheara 2022 zuwa ranar 29 ga watan Mayu.
A halin da ake ciki an samu mutane 66 masu ɗauke da cutar yayin da tuni cutar ta hallaka mutum guda.

Jihohin da aka samu ɓullar cutar sun haɗar da Kaduna, Delta, Neja, Rivers, Adamawa, da jihar Edo

Sauran jihohin su ne Oyo, Legas, Gombe, Bayelsa da babban birinin tarayya Abuja.
Hukumar ta ce an samu ƙaruwar yaɗuwar cutar a watan Afrilu.
Hukumar ta ce ta bza jami’anta domin tattara bayanai a kan mutanen da ake zargi su na ɗauke da cutar.