Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun kone wasu motoci Takwas akan hanyar Kaduna zuwa Birnin gwari a Jihar ta Kaduna.

‘Yan bindigan sun aikata ta’addancin ne a safiyar jiya Talata,kuma bayan faruwar lamarin ana kautata zaton ‘yan bindigan sun yi garkuwa da mutanen da ke cikin wasu motocin.
Mazauna garin sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun zo ne akan babura inda su ka budewa tawagar motocin wuta.

Shima wani mazaunin garin ya bayyana wa manema labarai cewa daga cikin motocin da ‘yan bindigan su ka sanyawa wuta ciki harda motocin gida, wasu kuma daga cikin fasinjoji sun samu nasarar kubuta daga hannun ‘yan bindigan tare da tserewa zuwa cikin daji.

Mazaunin garin ya ce har kawo yanzu ba su san adadin mutanen da ‘yan bindigan su ka yi garkuwa da su ba sakamakon babu wanda ya nufi gurin da abin ya faru.