A yayin da wani rikici ya barke a tsakanin wasu kungiyoyin ‘yan bindiga biyu a Jihar Zamfara sun hallaka wasu manya biyu daga cikin su da kuma yaran 15.

Lamarin ya farune a jiya Talata bayan bangaren shahararran dan bindigan Bello Turji ya zargi daya bangaren da hallaka mutum guda wanda ya kasance wani a karkashin yaron Bello Turji.
Wani da lamarin ya faru akan idonsa ya bayyana wa manema labarai cewa Bello Turji bayan ya yi garkuwa da wasu mutune daga bisani kuma ya kashe su.

Rahotannin sun bayyana cewa a lokacin da lamarin ya faru ana zargin daga cikin wadanda su ka rasa rayukan su ciki harda yaran Bello Turji yayin da wasu kuma su ka jikkata.

Harin wanda ya kasance harin daukar fansa akan kisan yaron Bello Turji.
Daga cikin manyan ‘yan bindigan da aka hallaka sun hada Dan Maigari da kuma Dulhu.