Kungiyar fulani makiya reshen kudu maso gabas ta tabbatar da kinsan ‘yan kungiyar mutum hudu da wasu ‘yan bindiga su ka yi a ranar Litinin a Jihar Anambra.

Shugaban kungiyar Alhaji Gidado Siddiki shine ya sanar da hakan a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Jihar.

Alhaji Gidado ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun hallaka mutanen ne a lokacin da su ka kai musu hari sansanin fulanin da ke Jihar.

Shugaban ya kara da cewa daga cikin wadanda ‘yan bindigan su ka hallaka gawar mutam biyu aka gani inda ya ce har yanzu ba a ga ta sauran biyun ba.

A yayin jawabin sa Alhaji Gidado ya ce ba wannan ne karon farko da ake kashe musu yan kungiyar su wanda kuma ba su san dalilin yi musu hakan ba.

Shugaban ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro a Jihar da su dauki mataki domin kawo karshen yawaitar kashe kashe mutanen a Jihar.

Sannnan ya bayyana cewa mutanen da ‘yan bindigan su ka hallaka sun hada Sale Idris Abdulmumin Sale Musa Idris da kuma Muhammad Sale.

Kakakin ‘yan sandan Jihar ya ce bai samu labaran samun harin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: