Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo Olu ya bayyana cewa dokar haramta hawa baburan Achaba da aka sanya a Jihar za ta fara aiki ne a yau Laraba.
Daga cikin kananan hukumomi shida da gwamnan ya haramta yin Achaban sun hada da Ikeja Lagas Island Apapa Surulere Lagos Mainland da kuma Eti-osa.
Sannan gwamnan ya bukaci jami’an tsaron yankin da su sanya idanu domin ganin dokar ta tabbata da kuma daukar mataki ga duk wanda ya karya dokar.
Gwamnan Jihar ya kuma tabbata da siyo kananan jiragen ruwa wanda shine zai maye gurbin baburan.
Itama anata bangaren rundunar ‘yan sandan Jihar ta sha alwashin daukar mataki akan dukkan wanda ya karya dokar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: