Ministan babban birnin tarayya Abuja Mommmed Bello ya umarci jami’an tsaro su kama duk wani da ya je belin mai laifi a wajensu.

Ministan ya bayyana haka ne a Abuja a yayin taron da kwamitin sadarwa da gwamnatin tarayya da ya shirya karo na 40.
Ya ce akwai ɓata gari da ake samun rahoton sakinsu a sassa daban-daban na Abuja bayan wasu sun tsaya musu.

Sannan ya buƙaci mazuna Abuja su sanar da mahukunta duk wani da su ka sani ya je karɓo wani mai laifi daga hannun jami’an tsaro.

Ministan ya ce tsarin shari’a na Abuja na cike da ƙalubale ganin yadda gidajen gyaran hali ke cike da masu laifi.
Ya ce a halin yanzu ana aike da masu laifi gidajen gyaran hali na Suleja a jihar Neja kafin kammala aikin faɗaɗa gidajen gyaran hali uku da su ke Abuja.