Hukumar jin daɗin alhazai a jihar Neja ta buƙaci maniyyata aikin hajji waɗanda ba su yi riga-kafin cutar Korona ba ba su gaggauta yi kafin lokaci ya ƙure.

Babban sakatare a hukumar Alhaji Umar Makun Lapai ne ya bayyana haka a wani taro da ya yi da jami’an hukumar a Minna babban birnin jihar.

Umar Makun ya ce ya zama wajibi maniyyatan da ba su yi riga-kafin cutar ba su gaggauta yi domin kaucewa haɗarin kamuwa da cutar.

Sannan ya shwarci maniyyatan da ba su kammala biyan kuɗin aikin hajjinsu ba su gagauta ƙarasa biya domin kaucewa jinkiri wajen tafiya.

Zuwa yanzu an ƙara wa maniyyatan wa’adin makonni biyu domin ƙarasa biyan kuɗin aikin hajjin bana.

Sannan hukumar ta ce a halin yanzu akwai gurbin matafiya ga maniyyatan da su ke da damar biya dmin gudanar da ibadar a bana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: