Wata kotu dake zaman a Ikeja ta Jihar Lagos ta yankewa wani mutum mai suna Anthony Abimoli hukuncin shekaru 24 a gidan gyran hali bisa damfara tare da satar kudaɗe kimanin Miliyan 71.

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa a Najeriya EFCC ita ce ta shigar da Anthony gaban kotun da tuhuma Tara.
An zargi Abimoli bisa sayar da Gas na damfara da mai dama siyar da filin wasu.

Sai dai bai musanta zargin da ake masa ba ya aikata hakan ne a Jihar Anambra.

Duba ga hujjoji da aka shigar a gaban kotu a kan wanda ake zargi bisa tuhumar sa da laifuka 9 tare da satar mukudan kudade wanda su ka kai kimanin miliyan 71 mai shari a Mojisola Dada ya yankewa mutum mai kimanin shekaru 73 a duniya hukuncin shekaru 24 a gidan gyaran hali.