Rahotanni daga filin taro na Eagle Square na babban birnin tarayya Abuja na tabbatar da cewar an kammala kaɗa ƙuri’ar zaɓen fidda ganin shugaban ƙasa.

Masu zaɓen sun kammala kaɗa ƙuri’unsu da misalin ƙarfe 7:45am na safiyar yau Laraba.

Bayan kammala kaɗa ƙuri’a an tsaurara matakan tsaro a wajen akwatunan zaɓen.

Yayin da ke kaɗa ƙuri’ar a daren ranar Talata, ƴan Takara bakwai ne su ka janyewa tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ja hankalin ƴan jam’iyyar da su zama tsintsiya maɗauri guda.

Bayan halartar wajen zaɓen da shugaban ya yi ya bar wajn bayan ƙarfe ɗaya na dare.

A na sa ran kowanne lokaci daga yanzu za a fara irga ƙuri’a tare da fitar da sakamako bayan kammalawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: