Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso ya samu tikitin takara a jam’iyyar NNPP.

A yayin babban taron da jam’iyyar ta gudanar yau a Abuja, daliget sun zaɓi Kwankwanso a matsayin wanda zai fito takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar NNPP.
Sanata Kwankwanso zai fafata a kakar zaɓen shekarar 2023.

Sanata Kwankwaso ya ce idan har ya zama shugaban Najeriya a shekarat 2023, zai inganta harkar ilimi, tsaro da kuma magance matsalolin talakawan Najeriya.
