Bayan lashe zaben fidda gwani wanda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi ranar Laraba, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyanashi a matsayin ɗan takarar da ya cacanci ya gajeshi wajen mulkin Najeriya.

Shugaban Najeriya Buhari ya bayyana haka ne a cikin saƙon taya murna ta ya fitar, wanda mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu.
Shugaba Buhari ya sha alwashin marawa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu baya, a yayin zaɓen shekarar 2023 mai gabatowa.

Sannan ya ce ya gamsu da ingancin Bola Tinubu wajen shugabancin ƙasa, ya ce zai ci gaba da bai wa demokaraɗiyya haƙƙin ta.

Shugaba Buhari ya ce a halin yanzu ya zama wajibi dukkanin ƴan jam’iyyar su dunƙule waje guda domin ganin sun sami nasara a zaɓen shekarar 2023.
Ya ce samun nasarar jam’iyyrsu a zaɓe na gaba, zai taimaka wajen ci gaba da yaƙi da cin hanci da rashawa, farfaɗo da tattalin arziƙi da kuma magance matsalar tsaro.