Rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa sun samu nasarar cafke mutane 24 wanda ta ke zargi ‘yan bangar siyasa ne a Jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Muyiwa Adejobi shine wanda ya aike da wata wasika ga manema labarai a Jihar.
Ya bayyana cewa jami’an tsaron sun samu nasarar ne a kauyen a Minki wanda ya ke kan hanyar Keffi zuwa garin Akwanga a wani Hotal bayan gama aikata ta’addancin.

Muyiwa ya ce wadanda aka kama yara ne ga wani dan siyasa wanda ya fito takara a shekarar 2023.

Sannan ya kara da cewa mutane su ka tayar da hankula a lokacin wani zaben fidda gwani da aka yi a Nasarawa ta yamma a Jihar.
Adejobi ya ce jami’an su sun kwato bindigogi guda goma da harsasai 37 wukake da kuma riguna guda hudu wanda harsashi baya fasawa da sauran wasu kayayyakin.
Muyiwa Adejobi ya ce za su aike da mutanen gaban kotu da zarar sun gama bincike a kan su.