Akalla mutane uku ne su ka rasa rayukan su wasu kuma su ka jikkata sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka a Jihar Katsina.

Jami’in yada labarai na Karamar Hukumar Abdulkarim Sani ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Lahadi.
Abdulkarim ya ce lamarin ya farune a daren ranar Asabar zuwa wayewar garin ranar Lahadi.

Jami’in ya kara da cewa ruwan saman da aka yi ya shafi wasu garuruwa biyu wanda su ka hada da Matsiga da Nasarawa da duk da ke cikin garin na Kankara.

Sannan ya ce an samu a sarar rushewar gidaje da dama a lokacin da ake ruwan.
Anata bangaren hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar SEMA ta hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Umar Muhammad ya sanar da faruwar Lamarin.
Umar Muhammad ya ce za ta gudanar da aikin kiddige a sarar da ruwan ya haifar.