Wasu da ake zargi “yan bindiga ne sun yi garkuwa da mutane Takwas a cikin jirgin ruwa a Jihar Bayalsa.

“Yan bindigan sun aikata ta’addancin ne a lokcin da mutanen su ke kan hanyar su ta komawa Jihar ta Bayalsa daga wani bikin binne gawa da su ka hallatta.

Jirgin ya debo mutane 15 ne daga cikin Karamar Hukumar Brass ta Jihar ta Bayalsa.

Wata majiya daga Jihar ta bayyana cewa mutane Bakwai daga cikin wadanda “yan bindigan su ka yi garkuwa da su sun samu nasarar tserewa “yan ta’addan.

Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Jirgin na Karamar Hukumar da “yan bindigan su ka yi garkuwa da su Daniel Bioduomiye shine wanda ya bayyana faruwar lamarin.

Daniel ya ce “yan ta’addan sun sace mutanen ne a kusa da wata gonar shinkafa a lokacin da mutane su ke kokarin komawa gida daga bikin binne gawar.

Anasa bangaren mai magana da yawun rundunar “yan sandan Jihar SP Asinim Butswat bayan ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce rundunar “yan sandan za ta zurfafa bincike domin cafko Maharan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: