Majalisar dokokin Jihar Kano ta amincewa gwamnan Dr Abdullahi Umar Ganduje da ya amso bashin naira biliyan 10 domin sayan kyamarar tsaro ta CCTV domin taimakawa a harkar tsaro.

Gwamnan Ganduje ya aikewa da majalisar wata wasika ne a zamanta na yau Laraba domin neman bayar da dama na amso bashin kudaden wanda shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya karanta.

A cikin wasikar da gwamnan ya aike ya bayyana cewa za a sanya kyamarorin domin inganta sha’anin tsaro da ke barazana ga Jihar musamman ma a wannan lokacin.

A zaman majalisar na yau majalisar bayan ta tattauna batun sannan ta yarjewa gwamnan da ya amso kudaden.

A cewar wasikar da ya aikewa majalisar sanya kyamarorin zai inganta sha’anin tsaro a Jihar da kuma dakile duk wani yunkuri na batagari da su ke san kawowa Jihar cikas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: