Gwaman Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya mika sunayen sabbin kwamishinonin 20 ga zauran majalisar dokoki ta Jihar domin tantance su kafin ya nada su.

Gwamnan ya mika sunayen ne a jiya Talata a yayin zaman majalisar, inda ya ce daga cikin wadanda ya mika sunayen su ciki harda wasu daga cikin tsoffin kwamishinonin da ya sauke.
Daga cikin mutane 20 din da gwamnan zai sake nadawa 17 daga ciki dukkan su tsofaffin kwamishinonin sa ne yayin da guda uku ne kadai su ka zamo sabbi.

Sabbin mutanen ukun da gwamnan ya zaba sun hada da Ali Bunu Mustapha Farfesa Muhammad Arabi da kuma Pogu Lawan Chibok.

Tsofaffin kwamishinonin su ne Adamu Lawan, Mustapha Gubio,Yarima Suleh,Lawan Wakilbe, Abacha Ngala,Kaka Shehu, Lawan Sugum, Sugum,Mele, Isa Haladu.
Sauran su ne Zuwaira Gambo,Babagana Malumbe, Tijjani Goni ,Yerima Kareto, Yuguda Saleh, Saina Buba,Abubakar Tijjani,Buba Walama.
A yayin wasu taruka da jam’iyyar APC ke gudanarwa dangane da gabatowar zaben fidda gwani na jam’iyyar ta APC a watan da ya gabata gwamnan Zulum ya sallami kwamishinoni 20 daga majalisar zartarwar Jihar.