Rundunar ƴan sandan jihar Benuwe ta kama mutane huɗu da ta ke zargi da hannu wajen kai hari ƙaiyen Igama a jihar.

Maharan sun kai harin ne a ranar Lahadi sannan su ka hallaka mutane 15 tare da ƙone wasu gidaje a garin.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Catherene Anene ya ce ɗaya daga cikin ƴan bindigan da su k akma ya mutu a sakamakon musayar wuta da jami’an staro.

Jami’an ƴan sanda sun ce sn haɗa kai da sauran jami’an staro tare da fara bincike a cikin dajin domin kama sauran mutanen da su ka kai harin.

Kakakin ƴan sandan ya ce sun samu nasarar kama mutanen ne a ranar Laraba yayin da su ke ci gaba da bincike domin kama sauran.
Bayan ɗaya daga cikin ƴan bindigan ya mutu a asibiti sun keɓe sauran mutane ukun waɗanda a halin yanzu su ke gudanar da binckike a kansu.
Hukumar ta buƙaci al’ummar ƙauyen Igama da su kwantar da hankalinsu sannan su bayar da dukkanin bayanan da su ke buƙata wanda hakan zai taimaka wajen samun nasarar aikinsu.