Shugaban ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) reshen jihar Kaduna, Ibrahim Ɗalhatu, ya yi Allah wadai da matakin korar malamai 2,357 a Kaduna bayan faɗuwa jarabawar cancanta.

Shugaban ya ayyana matakin da gwamnatin Kaduna ta ɗauka da saɓa wa doka.

A wata sanarwa da hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta jihar Kaduna (KADSUBEB) ta fitar ta hannun Hauwa Muhammed, ta ce hukumar ta gudanar da jarabawa kan Malamai sama da 30,000 a watan Disamba na shekarar da ta gabata.

Ta ce hukumar ta kori Malaman makarantun Firamare 2,192 ciki har da shugaban ƙungiyar NUT ta ƙasa reshen jihar bisa ƙin zama jarabawar gwaji da gwamnati ta gudanar.

A cewarta, Malamai 165 cikin 27, 662 da suka zauna jarabawar gwajin an kore su saboda basu samu cin jarabawar ba.

Sanarwar tace biyo bayan matsayar gwamnati na cigaba da gwajin Malamai domin inganta karatu ga yan Kaduna, hukumar ta sake gudanar da jarabawar gwaji a watan Disamba, 2021.

Kuma ya na daga cikin ƙa’idar hukumar ba’a buƙatar aikin Malaman da suka ci ƙasa da kashi 40 sai dai a sallame su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: