Yan sanda a jihar Zamfara, sun kwato bindiga kirar AK 47 guda 1 da alburusai 18 a yayin da aka kai sumame da su kauyen Saran Gamawa da ke unguwar Mata a ƙaramar hukumar Gummi ta jihar.

A ranar 19 ga watan Yuni na shekarar da mu ke ciki me dai rundunar ‘yan sandan da aka tura ta hanyar Gummi zuwa Bukkuyum ta samu labarin cewa ‘yan ta’adda dauke da makamai a kan babura sun mamaye kauyukan Saran Gamawa da Unguwar Mata da ke makwabtaka da kauyukan da nufin ta’addanci tare da sace mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Rundunar ‘yan sanda hadin gwiwa da ‘yan banga na kauyukan da lamarin ya shafa sun hada karfi da karfe tare da yin artabu da ‘yan ta’addan wanda aka dauki tsawon sa’oi ana yi.

Sakamakon haka, daya daga cikin ‘yan ta’addan ya ji rauni sosai, an kuma samu bindiga kirar Ak 47 a wurin, yayin da wasu da dama suka gudu cikin dajin da harbin bindiga daban-daban.

Kwamishinan ‘yan sanda Ayuba N. Elkanah ya yaba da jajircewar da ‘yan sandan suka yi tare da karfafa musu gwiwa da kada su gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane a jihar.
sannan kwamishinan ‘yan sandan ya umurci baturen ƴan sanda na Anka da ke makwabtaka da su tura jami’an su don ci gaba da sintiri a yankin.
Ko a makon da ya gabata sai da gwamnatin jihar ta bayyana yuwuwar sake katse layukan waya sanadiyyar yawaitar hare-hare da ake samu a jihar.