Wannan ke nuni da cewar sunayen shugaban ƙasa da mataimakansu da jam’iyyu su ka aikeea hukumar da su za ta yi amfani.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta bayyana cewar a cikin kundin dokokin hukumar babu inda aka basu damar sauya sunan yan takara da mataimakansu.

Kwamishinan zaɓe na ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama’a a kan katin zabe Festus Okoye ne ya bayyana haka a Abuja.

Ya ce sunayen yan takarar da aka aikewa hukumar da su za ta yi amfani kuma babu dokar da ta basu damar sauya sunayen yan takara ko mataimakansu.

Festus Okoye a hira da aka yi da shi a gidan talabiji na Arise ya ce wasu daga cikin yan takara sun aike da sunayen mataimakansu da nufin sauyawa gabanin lokacin zaɓe.

Idan ba a manta ba, jam’iyyar APC ta aike da sunan mataimakin shugaban kasa a matsayin na wucin gadi tare da nufin sauyawa a nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: