Tsohon ministan Neja Delta Godsday Orubebe ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

Ficewa tasa ta biyo bayan zaben fidda gwani na shugaban ƙasa da mataimakin sa wanda ake sa ran yi a shekarar 2023.
Tuni ya aikewa shugabannin jam’iyyar PDP a mazabarsa da ƙaramar hukumarsa wasikar ficewa daga jam’iyyar.

Orubebe ya ce jam’iyyar PDP ba ta shirya karɓe mulki daga hannun jam’iyyar mai mulki ba.

Bayan ficewar tasa, Orubebe bai bayyana jam’iyyar da ya koma cikin ta ba yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2023.
Idan ba a manta ba Orubebe shi ne wanda ya dakatar da bayyana sakamakon zaben shugaban ƙasa a shekarar 2015.