Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da kama wasu mutane 13 da ake zargi masu garkuwa da mutane ne a Jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar Sikiru Kayode Akande shine ya bayyana haka ga manema labarai.

Akande ya ce an kama mutane 13 ne bayan wasu bayanai da Jami an hukumar su samu na cewa akwai wadanda ake zargi da binne wasu makamai a wata unguwa, dililin daya sa su ka tsaura bincike cikin gaggawa tare da samun nasara.

Mutane 13 sun binne bindigu kamar Ak 47 karamar bindiga ta fiston da makudan kudade da kuma alburasai da dai sauran kayayyaki.

Mr. Sikiru ya ce yana matukar godiya ga jami’an yan sanda da na sa kai da ma alumma baki daya bisa kokarin ganin an samu wanann nassasara.

Sanann ya ci gaba da cewa ana nan ana ci gaba da bincike domin gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike a kansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: