Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta samu nasarar kuɓutar da jaridai biyu da wasu mutane 12 daga hannun masu garkuwa da mutane.

Mutanen su 14 a na zargin sun shafe fiye da kwanaki 40 a hannun yan bindiga.

Mai magana da yawun ƴan sandna jihar SP Muhammad Shehu ya ce sun ceto mutanen ne a wurare daban-daban da yan binsigan su ka killace su.

Kakakin ƴan sansan ya ce jariran biyu kowannensu shekararsa ɗaya.

Bayan samun bayanai a kan maɓoyar masu garkuwa da mutanen ƴan sanda haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro sun nufi karamar hukumar Tsafe tare da yi wa dajin Kunchi Kalgo ƙawanya tare da farwa yan bindigan.

Daga bayanan da utanen da aka kubutar su ka bayyana sun ce yan bindiga sun kai wani hari Nassarawar Wanke da ƙauyen Rijiya a karamar hukumar Gusau sannan su ka sace mutanen.

Kwamishinan yan sandan jihar Ayuba Elkanah ya danƙa mutanen ga yan uwansu sannan ya ce za su ci gaba da haɗa kai da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: