
Guda cikin manoman da su ka amfana da shirin bunƙasa noma da kiwo na jihar Kano KSADP ya bayyana cewar samar da tsarin ya taimakawa manoma tare da zamanantar da aikinsu.
Labaran Gadon Sarki da ke ƙaramar hukumar Warawa a Kano ne ya bayyana haka yayin wani taron nuna amfanin gona wanda shirin ya samar.

Shirin bunƙasa noma da kiwo na jibar Kano haɗin gwiwa da ƙungiyar SASAKAWA, ya koyar da manoma yadda za su inganta aikin gona da kiwo da kuma killace amfanin gona.

Daga cikin aikin da shirin ya yi, akwai horas da manoma yadda za su kiyaye lafiyarsu, da kuma basu iri mai kyau sai yadda za su shigar da amfanin gona kasuwa.
Haka kuma shirin ya horas da manoma yadda za su tafiyar da ayyukan gona a zamanance da kuma killace amfanin gona don gudun lalacewarsa.
Shugaban shirin bunƙasa noma da kiwo na jihar Kano ƙarƙashin SASAKAWA Abdurrashid Hamisu ya gamsu da nasarar da su ka samu sannan ya sha alwashin ci gaba da horas da mata da sauran manoma yadda za su tafiyar da ayyukan noma da kiwo a zamanance.
Taron da aka yi a ƙaramar hukumar Warawa ta jihar Kano ya samu halartar shugaban shirin da manoma da mata masu sarrafa amfanin gona.