Ƴan bindigan da su ka sace hakimin Panyam a jihar Filato sun sake shi bayan biyan kuɗin fansa naira miliyan goma.

A ranar Lahadi wayewar Litinin ƴan bindigan su ka yi garkuwa da hakimin a gidan sa yayin da su ka je dauke da muggan makamai.
Rahotanni sun tabbatar da cewar yan bindigan da su ka shiga garin sun haura su 20 sannan su ka yi ta harbin iska domin razana mutane.

Bayan garkuwa da shi tare da tafiya da shi maɓoya ƴan bindigan sun bukaci a ba su naira miliyan 150.

Sai dai daga bisani aka daidaita a kan naira miliyan goma kuma su ka sake shi a daren Laraba.
Ƴan uwan hakimin sun tabbatar da cewar sai da su ka biya naira miliyan goma kafin a sako shi.
Hakimin Panyam a karamar hukumar Mangu ya haɗu da ƴan uwansa bayan biyan kudin fansa.