Fittacen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya gargadi hukumomin tsaro game da kama matasan fulani barkatai da sunan yaki da ta’addanci.

Da ya ke magana a wurin taron kaddamar da Kungiyar Kare Hakkin Makiyaya a Kaduna, malamin ya ce kawo yanzu, akwai matasan fulani da yara da yawa wadanda ba su ji ba ba su gani ba a tsare.
Ya ce dalilin kafa kungiyar shine tabbatar da cewa matasan Fulani da ba su aikata komai ba sun samu adalci, ya kara da cewa za ta taimaka wurin kawo zaman lafiya a kasar.

Ya yi bayanin cewa cikin ayyukan kungiyar, akwai gano adadin yaran Fulani wadanda aka tsare su kuma ba su da laifi da neman lauyoyi da za su fitar da su.

Da ya ke magana kan kafa kungiyar, Shugabanta Farfesa Umar Labdo, ya ce kungiyar ba ta Fulani ne kadai ba, ta shafi dukkan makiyaya, daga kowacce kabila, yanki da addini.
Ya ce kungiyar za ta zama murya ga makiyaya da ba su da karfin fada a ji inda za su iya yi wa kasa bayanin matsalolinsu da bukatunsu da abin da suke fatan cimma.