Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun kone Ofishin ‘yan sanda da shaguna da gidaje a Jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis garin Zugu da ke cikin karamar hukumar Bukuyum ta Jihar.

Wani shugaban matasa a garin na Bukuyum Abubakar Garba ya bayyana cewa harin na ‘yan bindigan bai yi sanadiyyar rasa rayukan al’umma a yankin ba amma mutane da dama sun samu raunika.

Abubakar ya kara da cewa harin ‘yan ta’addan ya tilastawa wasu daga cikin mazauna yankin tserewa daga gidajen su domin tsira da rayukan su.

Shugaban matasan ya ce ‘yan bindigan sun kone gidaje guda uku da shaguna wadanda su ke makobtaka da Ofishin ‘yan sandan.

Shima wani basarake a yankin ya bayyana cewa jami’an na ‘yan sanda sun tsere kafin ‘yan bindiga su isa ga Ofishin.

Muhammad Shehu wanda ya kasan ce mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a Jihar bai ce komai ba dangane da faruwar lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: