Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa sun samu nasarar ceto mahaifiyar Alhaji Tijjani Ibrahim dan takarar sanata a Jihar Jigawa ta tsakiya Hajiya Fatima Ibrahim daga gurin wasu ‘yan bindiga da su ka yi garkuwa da ita garin Kano.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Lawan Shisu ne wanda ya bayyana faruwar lamarin ga manema labarai a garin Dutse babban birnin Jihar.
Kakakin ya ce lamarin ya farune a ranar Litinin a lokacin da ‘yan ta’addan su ka kutsa kai gidan mahaifiyar dan takarar sanatan wadda ta ke zaune a unguwar Tsangayawa da ke garin kiyawa a Jihar.

Lawan Shisu ya kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun samu nasarar kubutar da ita ne a karamar hukumar kunbotso cikin rukunin gidajen Danladi Nasidi da a Kano.

A yayin jawabin kakakin ‘yan sandan bai sanar da cewa an biya wadanda su ka sace ta kudin fansa ba ko bayan da su ka bukaci kudin fansar ko kuma sun yi artabu kafin su kubutar da ita.