Jami’an tsaron DSS a Jihar Nasarawa ta cafke wasu mutane da su ka bude wajen yin katin zabe na bogi a Jihar.

Jami’an sun kama mutanen ne a lokacin da su ke tsaka da damfarar mutane tare da amshe musu kudade da sunan za su yi musu katin zabe.

Mutanen sun bude guraren yin katin zabe na bogin a cikin kananan hukumomi 13 da ke Jihar.

Shugaba a sashen wayar da kan al’umma a hukumar zabe ta INEC a Jihar Ibrahim Anawo ya bayyana cewa ‘yan damfarar su na karbar naira 1,000 daga hannun al’umma da niyyar za su yi musu katin zabe.

Shugaban ya kara da cewa jami’an na DSS sun kama mutanen a makarantar sakandiren kimiyya ta gwamnatin Jihar da ke garin Lafiya a lokacin da su ke rabawa mutane fom din da za a yi musu katunan zabe.

Jam’in ya bayyana cewa an kama’yan damfarar ne a sakamakon wasu bayanan sirri da kwamitin da hukumar zaben ta kafa domin gano wadanda su ke karbar kudaden mutane da niyyar yi musu katin zabe.

Anawo ya ce ‘yan damfara sun shaida wa mutane cewa su na yin katin zaben ne hadin gwiwa da hukumar ta INEC da kungiyar su ta matasa don su yiwa mutanen katin zaben.

Ya ce a baya kungiyar ta rubuto takardar neman amincewa su hada gwiwa da hukumar amma hukumar ta ki amince musu daga bisa ni kuma su ka je su ka bude gurare su na karbar kudaden mutane da sunan yi musu katin zabe.

Ibrahim Anawo ya ce ‘yan damfarar su ne wadanda su ke batawa hukumar zabe suna inda ya ce hakan ba zai yuwu ba.

Shugaban ya ce jami’an hukumar ta DSS ta za su aikewa da ‘yan sanda mutane domin gudanar da bincike akan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: