Gwamnatin jihar Zamfara ta bai wa mazauna jihar damar mallakar bindiga a wani mataki na kawo ƙarshen ƴan ta’adda.

Gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle ne ya sahalewa mazauna jihar domin kawo ƙarshen ƴan bindiga a jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Ibrahim Dosara ya sanyawa hannu, gwamnatin ta ɗauki matakin ne ganin yadda ake samun yawaitar hare-hare a jihar.

Jihar Zamfara ita ce jiha ta biyu da aka bai wa mazauna jihar damar mallakar bindiga bayan jihar Katsina.

Tuni gwamnatin ta bai wa kwamishinan ƴan sandan jihar umarnin bayar da lasisi ga mutanen da su ka cancanta a ba su damar riƙe bindiga.

Hare-haren ta’addanci ya daɗe ya na faruwa a jihohin arewacin Najeriya wanda hakan ke silar salwantar da rayuwar mutane da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: