Jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun kai samame wani gida da ke unguwar Tudun Wada a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.

jami’an tsaro sun samu nasarar ceto matasa 21 da suka hada da almajirai.
Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), yayin da take tabbatar da faruwar lamarin, ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa wadanda aka ceto sun shaida wa kungiyar a lokacin da ake yi musu tambayoyi cewa an kawo su gidan ta karfi kuma suka koma Kiristanci.

Babban Sakataren Cocin Evangelical Winning All (ECWA), Rabaran Yunusa Nmadu, ya ce gidan da jami’an DSS suka kai wa sumamen ba abinda ake zarginsa da aikatawa ya ke ba, ya musanta cewa ana amfani da gidan ne wajen canzawa mutane addini.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an DSS sun kai samame gidan ne a ranar 14 ga watan Yuni, inda suka kwato wadanda aka kwashe, wadanda aka ce an kawo su Jos daga wata jiha.
Samamen da aka kai gidan, a cewar Daraktan kungiyar agaji ta JNI reshen jihar Filato, kuma babban jami’in tsaro na babban masallacin Jos, Danjuma Khalid, ya zo ne bayan daya daga cikin wadanda abin ya shafa mai suna Abdulrahman Usaini, wanda ya tsere daga gidan, ya kawo rahoton cewa an kama su, ya zauna a gidan har tsawon wata takwas.
Abdulrahman wanda dan asalin garin Azare ne a jihar Bauchi ya ce an kai shi garin Gombe domin yin karatun Alkur’ani, daga nan aka kai shi Cocin ECWA da ke Jos kuma aka tilasta musu sauya addini.