Gwamna jihar Imo Hope Uzodinma na jihar Imo, ya ba ‘yan bindiga da suka hana zaman lafiya wa’adin kwanaki 10 su miƙa wuya.

Gwamna Uzodinma ya shawarci ‘yan bindigan su bar dazukan jihar kuma su miƙa wuya tare da damƙa makamansu ga Sarakunan gargajiya don a yafe musu.
Da yake jawabi ga manema labarai a Owerri, Gwamnan ya ce jihar Imo zata karɓi bakuncin bikin shekara-shekara na sojojin Najeriya daga 30 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Yuli.

A cewarsa, akalla dakarun tsaro 10,000 daga hukumar sojojin ƙasa, na sama da na ruwa da kuma yan sanda, zasu halarci bikin.

Gwamnan ya ƙara da cewa jihar Imo zata karɓi sabbin kayan aikin jami’an tsaro, waɗan da za a yi amfani da su wajen share ƴan bindiga a wuraren da suke ɓuya cikin dazuka daban-daban a faɗin jihar.
Uzodinma ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ake tsammanin zai buɗe bikin ranar ta Sojoji, ya zaɓi ranakun 12 da 13 ga watan Yulin domin buɗewa da wasu ayyuka.
A cewar gwamnan shugaba Buhari zai buɗe hanyoyin Owerri-Orlu da Owerri-Okigwe, kana ya kaddamar da fara aikin hanyar Owerri-Mbaise-Umuahia (daga hukumar kashe gobara) da hanyar Orlu-Akokwa.