Daga Yahaya Bala Fagge

 

Gwamantin Jihar Zamfara ta sanya dokar hukuncin kisa ga duk wani dan bindiga da aka kama.

Wannan yana cikin wani kudiri da majalissar dokokin Jihar ta Zamfara ta yi wanda ake ganin a yau Talata Gwamna Bello Matawalle zai saka hannu akan dokar.

Gwamnan ya aikewa majalisa dokar hukumcin kisa ga duk ɗan bindigan da aka kama a jihar.

Babban mataimakawa Gwamnan Abdullahi shinkafi shine ya bayyana haka ga manema labarai a yau Talata.

Ya ce dokar za ta yi aiki ga duk wanda aka kama da laifin ta’adanci ko ya ke kai wa ƴan bindiga bayanai sirri.

Idan ba a manta ba a karshen makon nan ne Gwamnati Jihar Zamafara ta bayar da dama ga kowanne mazaunin jihar ya mallakin bindiga domin kare kai daga hanun yan bindiga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: