Kungiyar kwallon kafa ta Manchaster united ta bayyana kwadayin daukar dan wasan Napoli dan asalin kasa Najeriya wato Victor Osimeh

Jaridu sun bayyana cewa tuni Manchester ta shiga tattaunawa da Napoli domin ganin ta dauki dan wasan karkashin jagorancin Erik Ten Hag.
Manchester United ta kasa kai bantenta a wannan kakar da aka yi bankwana da ita har ta ke neman dan wasa zai yi kokari ganin K
Kungiyar ta dawo da karkashin ta.

Kungiyar ta Manchaster wadda ke rake a matsayin garzuwar gasar Primier kasar England ta fafata wasanni 38 da cin kwallaye 57 inda gwarzon dan wasan ta Cristiano Ronald ya zura 18 cikin wasa 30 da yayi.

Kuma kungiyar ta yi rashin yan wasa kamar Cavani Lingard da kuma Juan Mata sakamakon karewar kwantaragin su da ya kare.
Dan wasa Victor Osimeh ya sanyawa kungiyar Napoli hannu a shekarar, 2020 akan kudi Euro Miliyan 70, sannan ya ci kwallaye 18 a wasani 32 tare da taimakawa aka ci shida a kakar da ta wuce.