Yara sama da 3,000 ne ba sa zuwa makaranta daukan Karatu sakamakon hare haren yan bindiga a karamar hukumar Jibiya ta Jihar Katsina.

Wannan ya fito ne daga bakin shugaban yan gudun hijira na karamar hukumar Jibiya sa’ad salihu, ya ce akalla akwai yara da ba sa zuwa makaranta sakamakon yawaitar harin yan bindiga a yankunansu.

Sa’ad ya ce a baya yaran su na zuwa makaran sai dai bayan hari da yan bindigan suke kaiwa yankunansu ya hanasu ci gaba da zuwa makaranta.

Ya ƙara da cewa mafi yawan yan hijiran sun fito ne daga yankin Zango Shimfida Kwari Tsauni Far Faru Tsambe da Gurbin Magariya.

Salisu ya ce wannan babban koma baya ne ga ilimi ya zamana akwai yara sama da 15,000 wadanda baza su zuwa makaranta.

Kuma dadin na ci gaba da ƙaruwa sannan an samu mutuwar Mata 23 wadanda takaici ya kashe a wanann wuri da kuma samun haihuwar mata 35.

Leave a Reply

%d bloggers like this: