Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya sanya hannu akan wata sabuwar doka wadda za ta yi aiki akan masu aikata manyan laifi ciki harda ‘yan bindiga.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya Talata wanda su ka bayyan sanya hannu a dokar ta fara aiki, kuma sabuwar dokar ta tanadi hukuncin kisa ta hanya raya ga ‘yan bindiga da masu aikata laifuka makamantan haka a Jihar.

A yayin jawabin gwamnan Bello Matawalle bayan kammala sanya hannu a dokar ya bayyana cewa dokar za ta yi aiki ne don ganin an yaki ‘yan bindiga masu garkuwa da mutune da satar shanu a Jihar.

Bello Matawalle ya kara da cewa gwamnatin sa za ta sanya idanu akan dokar domin kula da rayuka da dukiyoyin al’umma a Jihar.

Gwamnan Bello Matawalle ya ce gwamnatin sa za ta samar da wasu hanyoyi inganta al’amuran tsaro a Jihar nan gaba.

Matawalle ya bayyana cewa wadanda su ke sukar damar da aka bai wa jama’ar jihar na kare kansu daga harin yan bindiga, ya ce akwai bkatar yin duba akan halin da Jihar ke ciki na yawaitar hare-haren ‘yan bindiga tare da yin garkuwa da mutane da jikkata su.

Gwamnan ya kuma ce dokar ta bayar da damar hukunta wadanda su ke taimmakawa ‘yan bindiga wajen kai hare-hare da kuma daurin rai da rai ko kuma daurin shekaru 20 ko 10 ba tare da zabin biyan tara ba ga wadanda aka kama su na taimakawa ‘yan bindiga.

Sannan kuma gwamna ya jinjinawa majalisar don tabbatar da ayyukan su.

Majalisar dokokin Jihar ta Amince da kudirin sanya dokar ne a ranar 27 ga watan Yunin da mu ke ciki

Leave a Reply

%d bloggers like this: