Wata babbar kotun tarayya a jihar Oyo ta yankewa wani da aka samu da aikata damfara hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekaru 235,

Hukmar hana cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ce ta gurfanar da Olatunji bayan sun kamashi da aikata damfara a yanar gizo.

Tun a watan Yulin shekarar 2019 aka kama Olatunci tare da fara bincike a kan laifuka 45 da ake zarginsa da aikatawa.

Bayan kammala bincike daga hukumar, sun gurfanar da matashin a gaban babbar kotun tarayya ta jihar.

Yayin da aka gurfanar da Scales Olatunji a gaban kotu, matashin ya musanta zargin da ake yi a kansa bisa laifuka 45 d ake tuhumarsa a kai.

Daga ƙarshe mai shari a Agatha Okeke ya yanke wa matashin hukuncin zaman gidan yari na shekaru 235.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: