Yan sa kai sun hallaka yan bindiga Tara bayan wata bata kashi da aka yi tsakanin su yan sakai na bijilanti.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a kauyen Zak karamar hukumar Wase ta Jihar Filato.
Wani shaida ya ce fafatawar ta yi sanadiyyar mutuwar yan bindiga Tara yayin da yan bijilanti uku su ka rasa rayukansu.

Wani jami’in soja ya bayyana cewa yan bindigan sun kai harin ne yayin da Sojojij suka ta fi fatattakar wasu yan bindiga a wani kauye.

Yan bindigan wadanda su ka bayyana kai hare hare a kauyukan Sabon Zama, Gidin Dutse, anguwan Tsihuwan soldier.
Sannan akwai Anguwan Yuhana da Anguwan Mangu duk dake karamar hukumar Wase ta Filato.
Jihar Filato jiha ce dake arewacin Najeriya sunanta ya fara bayyana a yan kwanakin nan bisa rashin tsaro da take fuskanta na hare-haren ƴan bindiga.