Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kai hari majalissar dokokin Jihar Bauchi tare da raunata mutane Shida da kuma lalata kayayyaki.

Harin wanda aka kai jiya Litinin ya yi sanadiyyar raunata mutane Shida tare da farfasa tagogi da sauran kayyakin anfanin majalissar.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito ya nuna cewa yan bindigan su isa majalisar a jiya Litinin da misalin karfe 4:00 na yamma yayin da yan majalissar ke gudanar da wani taro.

Babale Abubakar Daya daga cikin yan majalissar ya bayyana cewa yan bindigan sun je da manyan bindigu wanda suka kai 100 tare wasu makaman.

Sannan sun raunata mutane Shida tare da lalata wasu motoci bayan dukkansu su sun fita a guje.
Abubakar ya ce mutanen da lamarin ya rutsa da su tuni an garzaya da su asibiti tare da karbar magani.
Gwamnan Jihar Bauchi ta bakin maitaimakamasa ya ce bayyana harin a matsayin abin takaici kuma gwamanti ta na bayar da umarni ga hukomomin da su tabbar sun gudanar da bincike tare da kamo wadanda ake zargi sun kai harin.