Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya sun ce a shirye su ke su janye yajin aiki da su ke yi muddin aka sauraresu.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa Farfesa Emmanuel Osodoke ne ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da gidan talabiji na Channels.

Ƙungiyar ta zargi gwamnatin tarayya a kan rashin mutunta yarjejeniyarsu.

Ya ce a shirye su ke su janye yajin aikin da su ke yi ko gobe.

Farfesa Emmanuel Osodoke ya ce, sun zuba ido su ga matakin da gwamnati za ta ɗauka don ganin yajin aikin ya zo ƙarshe.

Sannan ko da za a ƙulla yarjejeniya za su amince da hakan ko da zaman zai kasance a yau.

Ya ƙara da cewar sun kammala cimma matsaya illa sanya hannu a yarjejeniyar da aka tsaya a kanta ne kadai ya rage wanda a yanzu su ke jiran gwamnatin.

Shugaban ya ce watanni biyar ke nan su ka shafe ba tare da ana biyan malaman jami’ a albashi ba.

Idan ba a manta ba ƙungiyar ASUU ya shiga yajin aiki ne domin neman wasu hakƙoƙinsu daga wajen gwamnatin tarayya wanda har yanzu ba a kai ga kawo karshen sa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: