Rahotanni daga jihar Katsina na tabbatar da cewar ƴan bindiga sun kai wa ayain tawagar shugaba Buhari hari a jihar Katsina.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na kan hanyarsa ta zuwa Katsina domin gudanar da bikin babbar salla a birnin Daura.

Mai magana da yawun shugaba Buhari Malam Garba Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin a daren Talata kamar yadda jaridar Daily Nigeria ta ruwaito.

An kai wa shugaban hari ne a Dutsin-ma ta jihar Katsina kuma ake zargin mutane biyu daga cikin tawagar sun jikkata.

Sai dai jami’an tsaron da ke tare da shi sun daƙile harin yayin da tuni shugaban ke Daura cikin ƙoshin lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: