Yan ta’ddan kungiyar Ansaru da suka tare jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a kwanaki, suka dauke fasinjoji, su na barazanar kashe wadanda su ke tsaren.

Daily trust ta rahoto cewa ‘yan ta’addan sun yi magana cewa idan ba a biya masu bukatunsu ba, za su dauki fansa a kan wadanda suka kama.

Wani sakon sauti yana yawo a halin yanzu, a ciki aka ji wani a cikin wadanda ‘yan kungiyar ta Ansaru suka rike, yana cewa za a yanka sauran da ke tsare.

Wannan mutumi yake cewa tun da har gwamnatin tarayya ba ta biyawa ‘yan ta’addan bukatunsu ba, sun dawo ta kan su, su na barazanar cewa za su yanka su.

Tukur Mamu ya tabbatar da ingancin fai-fen, ya kuma ce shakka babu, ‘yan ta’addan sun zabi yau (Laraba) a matsayin ranar da za su soma wannan danyen aiki.

Alhaji Tukur Mamu yana cikin wadanda suka zama sila tsakanin gwamnati da ‘yan ta’addan.

Mamu ya shaidawa Daily Trust cewa shi ya roki ‘yan ta’addan da su yi hakuri, su nemi bukatunsu a wajen ‘yanuwan wadannan Bayin Allah da suke hannunsu.

Bayan Mamu ya nemi alfarma, sai suka bukaci ayi hakan ganin cewa gwamnati ta na bata lokaci. Amma sun ce idan suka ji shiru a nan ma, za su fara kashe su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: