Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya shiga wata ganawa da shugabannin tsaro da ministoci a fadarsa da ke Abuja a safiyar yau Juma’a.

Ganawar na zuwa ne bayan kai hari gidan yari na Kuje da kuma tawagarsa da aka kai wa hari a Katsina.
A na zargin batun da za a tattauna. a nasaba da farmakin da yan ta’adda suka kai gidan gyara hali na Kuje a Abuja.

Harin gidan yarin da aka kai ya nuna cewar fiye da fursunoni 600 ciki harda mayakan kungiyar Boko Haram ne suka tsere a yayin harin.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, shugaban hafsan sojin ƙasa Laftanal Janar Farouk Yahaya, shugaban sojin sama, Air Marshall Isiaka Amao, shugaban sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo da Sufeto Janar na yan sanda, Alƙali Usman Baba.
Yan majalisar shugaban kasa da su ka halarci taron sun hada da ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, takwaransa na harkokin yan sanda, Mohammed Dingyadi.
Sai ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami.
A gefe guda, an ji cewa Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta bayyana neman wasu kasurguman mutane 64 ruwa a jallo daga cikin wadanda suka tsere daga fashin gidan yari na Kuje ta babban birnin tarayya Abuja.
Dangane da bayanin da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abubakar Umar ya fitar, wadanda suka tsere an ce ‘yan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ne.
Idan ba a manta ba, an samu hargitsi yayin da wasu ‘yan ta’adda suka farmaki gidan yarin tare da sakin fursunoni daruruwa.