Rundunar yan sandan jihar Nassarawa ta bayyana cewa ta kama wani ɗan ƙungiyar Boko Haram da ya gudu daga gidan gyaran hali na kuje dake babban Birnin tarayyar Abuja.

An kama Hassan Hassan a babban Birnin Jihar na Lafiya.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar DSP Rahman Nansel shi ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Nansel ya ce mai kwamishinan yan sandan jihar ya bayar da umarnin kai wanda aka kama zuwa babban sashen tsaro kafin mika shi ga hukumar gidan gyaran hali.

Sannan ya ce ya na da tabbacin zai kama sauran wadanda ake zargi sun tsere zuwa jihar nan da ba da jimawa ba.

Idan ba a manta ba a makon da mu ke bankwana da shi ne kungiyar ISWAP ta kai hari gidan yari da ke Kuje a Abuja babban Birnin tarayyar, kuma ake zargin masu laifi akalla 800 tsere daga gidan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: