Rundunar yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da kubutar da wani dan asalin kasar china wanda aka yi garkuwa da shi a kwanakin baya.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar SP Ajayi shi ne ya bayyana ga mena labarai.

Ya ce an samu nasarar kubutar da dan Chinan sakamakon yan sanda da suka tsaya a dajin ba dare ba rana.

Ajayi ya ce an kubutar da dan China sannnan an yi masa gwajin lafiya kuma daga bisa aka mika shi ga iyalan sa.

Wasu da ake zargin masu garkuwa ne su ka yi garkuwa da wani mutum dan asalin kasar China a ranar 3 ga watan Yuli a kan babbar hanyar Olu a Jihar Kwara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: